Antisa Keyar Matashin Daya Batawa Mai Dakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari "Suna" Kotu

 Ana zargin Aminu da wallafa Wani Rubut Da Yayi A Twitter Wanda Ake Ganin Cin Mutunci Ne Da Yayi Wa Uwar Gidan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.







29 November 2022

'Yan ajin su Aminu Adamu, ɗalibin da ake zargi jami'an tsaro sun Cafke Shi kan zargin cin mutuncin matar shugaban Nigeria bayan Yayi wani Posting A Twitter

 Iyayen Aminu Ne Suka Bayyanawa BBC labarin yadda abin ya faru.


Labarin Bacewar Aminu ya soma Bayyana ne a karshen Satin jiya bayan 'yan ajinsu Jami'ar Tarayya da ke Dutse a Jihar Jigawa, sun yiwa Iyayen Aminu korafin daina ganinsa, Wanda iyayensa sun soma bincike don neman abin da yafaru Da Dansu.


Sai daga baya Aminu ya kira iyayensa a waya yana Fada musu cewa yana hannun jami'an tsaro a Abuja bisa zargin Posting Din Da Yayi A Twitter kan matar Shugaba Muhammadu Buhari.











Kabiru Korial, Wani Abokin Shi Kuma Dan Aji Su Alameenkamar Ne yadda suke kiran Aminu, ya ce tare suke da abokin nasa tun shekarar farko ta karatunsu har zuwa yanzu da suke shekarar karshe a sashen Kula Da  Tsaftar Muhalli



Alameen Yana Da Kokari Sosai A Cikin Dalibai Masu Kokari A Aji Yana Daya Daga Cikin Su Inda sakamakonsa yake kan daraja ta biyu wato 2:1 tun da muka soma karatu, bai taɓa Faduwa ko fuskantar Rashin nasara a jarrabawa ba in ji Wani Abokin Karatunsa Kabiru.


Wani abin burgewa Da Alameen Din shi ne Yana son barkwanci da tsokanar mutane  kuma mutumin kirki ne ba shi da matsala, bai taba samun matsala da kowa ba In Ba Yanzu Ba.







Wani Abokin Aminu Kuma Dan Aji Su, Prince Ahmed Amoeva, ya Bayyana kalamansa sannan ya kara da cewa a ajinsu mutane sun saba da shi sosai, ana sonsa kuma yanzu haka ana ta addu'ar a sake shi don ya dawo ya rubuta jarrabawarsu ta karshe da za a Fara a Sati Mai Zuwa.

Previous Post Next Post