Kalli Sababbin Kudaden Nigeria Da Aka Canjawa Fasali Daga #200 #500 #1000

 A Yau Ne Shugaban Kasar Nigeria Mai Girma Muhammadu Buhari Ya Kaddamar Da Sababbin Kudaden Da Aka Canja Daga Naira Dari Biyu (200) Da (500) Dakuma (1000).

An Kaddamar Da Sababbin Kudin Ne Ayau A Fadar Shugaban Kasa Dake Garin Abuja Aso Rock Inda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ne Da Shugaban Banki Nigeria Suka Kaddamar Dasu.







Babban Bankin Nigeria Wato Central Bank Of Nigeria (CBN) Yace Daga Ranar 15 Ga Watan December Shekarar Nan Zai Sake Domin Fara Amfani Da Kudaden.







Zakuma A Daina Amfani Da Tsofaffin Takardun Kudaden Daga Ranar 31 Ga Watan January Shekarar 2023 Wanda Wannan Wa'adin Na Daina Amfani Dasu Na Nan Daram Kamar Yadda Gwamnan Bankin Godwin Emefele Ya Fada A Bikin Kaddamar Da Sababbin Kudaden Yau A Fadar Shugaban Kasa.

Previous Post Next Post