Kalli Bidiyon Gidan Galar Da Yan Hisba Suke Nema Ruwa A Jallo Saboda Wannan Lalatar Da Akayi

Hukumar Hisbah ta ka kai sumame wani katafaren gidan da ake tara matasa maza da mata, ana aikata badala da shan Shisha a daren Talata.

Wata takarda mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar ta Hisba, Lawan Ibrahim Fagge, aka kuma rabawa manema labarai, ta bayyana cewar, Dakarun na Hisbah sun isa gidan sun Tatar da gidan ya dinke da irin wadannan matasa, a unguwar Nassarawa, kan titin sulaiman Crescent, suna tsaka da tafka badala.

Sanarwar ta kuma ce, Jami’an Hisbah sun sami nasarar cafke mutane 53, Wanda ya hadar da mata 26 da maza 27, a halin yanzu sun shiga komar Hisbah.


Previous Post Next Post