Yadda Wata Matar Aure Ta Samu Ciki Ba Tare Da Ta Kwanta Da Mijinta Ba


Wata mata mai neman saki a gaban kotu, Taibat Abubakar, ta gaya wa kotun majistare mai zamanta a Ipata cikin birnin Ilorin na jihar Kwara, cewa ba ta san yadda aka yi ta samu juna biyu ba.

Taibat ta bayyana cewa ba za ta iya yin bayanin yadda ta samu juna biyu ba tun da ba ta yi kwanciyar aure ba da mijinta, Mr Salihu Abubakar, cewar rahoton Daily Trust.

A kalamanta: “Ya ce na aure shi amma na ce aa saboda bana son shi. Amma ya nace inda ya ce sai na aure shi ko ina so ko ba na so.”

“Kwatsam kawai wata rana sai ya kirani yake cemin ina ɗauki da juna biyunsa kuma kada na kuskura na zubar da shi. Duk da na yi mamaki amma ban ɗauki abun da gaske ba har sai da na ga jinin al’ada ta bai zo ba a ƙarshen wata duk da cewa ba mu yi kwanciyar aure da shi ba.”

“Ya biya kuɗin sadakina kuma na haifar masa yaro ɗaya, amma yanzu ban ƙaunar shi kwata-kwata.”

Taibat, wacce ta nemi kotun da ta raba aurensu, ta buƙaci ya riƙa biyanta kuɗin ciyar da yaron N10,000 duk wata, sannan ta kuma kotun da ta sanya mijin na ta ya riƙa biyan kuɗin makarantar yaron.

Mijin ya musanta bayanin da matarsa ta yi a gaban kotu

Salihu ya musanta bayanan da Taibat, inda ya ce da farko ba ta karɓi tayin da ya zo mata da shi ba amma daga baya sun daidaita kansu.

“Mun yi kwanciyar aure da ita cikin hankalinmu ba a cikin mafarki ba ko sihiri kamar yadda ta ke cewa.”

A cewarsa.. Majistare Ajibade Lawal, ta gayawa ma’auratan cewa su tsaya a yadda su ke har sai zuwa ranar da za a cigaba da sauraron shari’ar ta 25 ga watan Yulin 2025.

Previous Post Next Post