Shin idan mutum zai shiga fim ridda yake ko fita daga musulunci yake ?- Jaruma Kyauta dalaliya


Fati nayo fulanin asaline wanda anka fi sani da Kyauta dillaliya tayi wani ga jerin bidiyo wanda takw shiga tambaya ga manya manyan jaruman masanantar kannywood.

Fati nayo itama jaruma ce kada ku manta da wannan amma sai ankaji tana furta wannan kalamai a cikin wani faifan bidiyo da ta wallafa inda ta jefa tambayar ga Ali nuhu da Adam a zango domin sune Ali Nuhu ana masa kallon sarkin kannywood baki daya inda shi kuma Adam a zango mataimakin sa kamar yadda take furta ga tambayar nan.


Shin idan mutum zai shiga fim ridda yake ko fita daga musulunci yake ?- Jaruma Kyauta dalaliya

Ina Ali nuhu shugaban yan fim na Nigeria baki daya, ina adam a zango mataimakin ka ko ana so ko ba’a so kuna akan gaba ina furodusas dinku , ina daraktan dinku zo in tambayeku.

Shin idan mutum zai shiga fim ridda yake ko fita daga musulunci baki daya? Ni naga wani mutum kwanakin baya ya fito yana cewa ya daina fim ya daina waka naji yana sabunta kalma shahada, kai mai tuba idan zaka tuba ka tashi karshen dare Allah yana saukowa yana waye mai neman gafara in gafarta masa ba zuwa zakayi ba dan mutane su sani ba.

Shin ka tabbatar da fim ne kawai saɓon da kake nifa nasan nifa na rantse da Allah ni fati nayo nayi nadamar shiga fim, saboda kullum zagin yan fim ake ana aibanta mu muna da yaya da juri’a inji ta fati nayo.”

Lallai wannan jarumar ta aika da sako babba ga wadannan jarumai.

Ku kasance da mu domin jin shin zata samu amsa daga wajensu ko kuma wasu jaruman da ke cikin Masana’atar Kannywood din .

Previous Post Next Post